1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zanga a kasar Chadi

Ibrahim SaniNovember 8, 2007
https://p.dw.com/p/C5ac

Daruruwan mutane a Chadi na gudanar da zanga zangar adawa da Gwamnatin kasar.Masu zanga zangar na zargin Gwamnatin ne da sakin Turawan nan da sukayi ƙokarin ficewa da yarar nan 103 daga kasar.A cewar masu zanga zangar, dole ne gwamnati ta dawo da Turawan tare da gurfanar dasu a gaban ƙuliya.Rahotanni sun rawaito cewa, masu zanga zangar na ɗauke da kwalaye a hannayensu,dake ɗauke da rubuce rubucen Allah wadai da Shugaban Faransa, Mr Nicolas Sarkozy.Masu Zanga zangar na zargin shugaban na Faransa ne da hannu a cikin sakin Turawan.A makon daya gabata ne dai, aka zargi Turawan su tara da ƙoƙarin safarar yaran 103 izuwa kasar ta Faransa.