Zanga zanga a Jamus | Labarai | DW | 08.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zanga a Jamus

A yau an shiga kwana na uku na yajin aiki a jihar Baden-Würtemberg dake kudancin Jamus.

Dubban maaikatan kwashe shara da jamian asibiti da kuma maaikatan gidajen kula da yara kanana,suna yajin aiki ne saboda shirin gwamnatin jihar na kara tsawon lokacin aiki daga saoi 38 da rabi zuwa saoi 40.

Hakazalika akwai alamun shiga wani yajin aikin a masanaantun sarrafa karafa da kuma na hasken wutar lantarki,yayinda suka fara muhawara a yau laraba,game da karin kashi 5 cikin dari na albashinsu,wanda masu masanaantun suka ce yayi yawa.