Zanga zanga a Jakarta | Labarai | DW | 03.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zanga a Jakarta

Jamian yansanda na cigaba da harba barkonon tsohuwa wa dubban jamaa dake zanga zanga a birnin jakartan Indonesia,domin bayyana adawa da shirin gwamnatin kasar na yiwa dokokin aiki gyaran fuska.shugabannin harkokin kasuwanci a Indonesian dai sun bayyana sabon tsarin da rashin dacewa,saboda zai kori masu zuba jari a harkokin ciniki a cikin kasar daga ketare.Gwamnatin kasar na kokarin yiwa dokar aiki gyaran fuska ,domin bawa masu daukan maaikata damar daukan matakai na ladabtarwa,hana yajin aiki tare da saukaka biyan kudaden wadanda aka kora daga bakin aiki.Kusan mutane dubu 30 sukayi jerin gwano akan titunan birnin na jakarta ayau,wanda ke zama zanga zagan baya bayan nan a jerin bore da alummar indonesia keyi na bayyanawa gwammati adawarsu da dokokin kwadagon da ake shirin yiwa gyaran fuska.