Zanga-zanga a Ireland. | Labarai | DW | 27.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Ireland.

An gudanar da zanga-zangar nuna adawa da shirin tsuƙe bakin aljiu a Ireland.

default

'Yan zanga-zanga A Ireland

Ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar Ireland na gudanar da zanga-zanga domin nuna damuwa da tsarin da gwamnatin ƙasar ta amince da shi na tsuƙe bakin aljihu. Mutane kamar dubu 50 ne suka bazu akan titunan Dublin babban birnin ƙasar. A farkon wannan mako ne gwamnatin ta ƙasar Ireland ta gabatar da tsarin kasafin da ta na cike giɓi a tsawon shekaru huɗu wanda zai samar wa ƙasar da kuɗaɗe biliyan dubu 15. Sai dai a sakamakon wannan tsari gwamnatin za ta rage kuɗaɗen fansho da na albashi tare kuma da ƙara kuɗaɗen haraji.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita: Halima Balaraba Abbas