Zanga-zanga a Faransa | Labarai | DW | 20.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Faransa

A Faransa Ƙungiyoyin ƙwadago sun shiga kwana na bakwai na yajin aikin gama gari

default

Zanga-zanga a Faransa

A ƙasar Faransa ƙungiyoyin ƙwadago sun shiga kwana na bakwai na yajin aikin gama gari,domin nuna adawa ga shirin gwamnati na ƙara yawan shekarun ritaya daga shekaru 60 zuwa 62.

Masu zanga-zangar sun giggilma manyan motoci bisa tituna.Wanan mataki ya kawo cikas matuƙa wajen  zirga zirga, zuwa filayen saukar jiragen sama, da kuma tashoshin ajiyar makamashi.

Wannan mataki ya haddasa ƙarancin man fetur a ƙasar domin kashi ɗaya cikin uku na gidajen mai ƙayau su ke.

A yayin da ya ke jawabi game da matsalar ministan ciki gida Brice Hortfeux ya ce gwamnati za ta ɗauki matakan da su ka dace domin maido doka da oda.

" Za mu yi belin dukkan  runbuna adanon mai, domin ba daidai ne ba ´yan tsirarun mutane su juya mafi yawan jama´a yadda su ka dama".

A cewar ƙungiyoyin ƙwadago mutane miliyan ukku da rabi su ka hallara a zanga-zangar jiya, amma a lissafin gwamnati, mutanen ba za su wuce miliyan ɗaya da ´yan ka ba.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Mohammad Nasiru Awal