Zanga-zanga a Faransa | Labarai | DW | 05.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Faransa

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bani Adama sun zargi Sarkozy da wuce gona da iri ta fannin matakan tsaro

Ƙungiyoyin ƙwadago da na kare haƙƙoƙin  bani adama sun shirya wata gagarumar zanga- zanga a ƙasar Faransa, domin nuna adawa ga abin da su ka kira wuce gona da iri da shugaban ƙasa, Nikola Sarkozy ke yi, ta fannin matakan tsaro.Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai ga matakin da gwamnatin Faransa ta ɗauka, wajen kora romawa ´yan kaka gida, zuwa ƙasashensu na asuli, mussamman Rumaniya da Bulgariya.

A ɗaya wajen, sun ƙalubalanci dokar da ta tanadi ƙwace takardar zama cikkaken ɗan ƙasar Faransa, ga mutumen da aka samu da lefin kai hari ga jami´an tsaro.

Ranar Talata mai zuwa idan Allah ya kai mu,Sarkozy zai fuskanci wani saban ƙalubale daga Ƙungiyoyin ƙwadago, wanda su ka ƙuduri shiga yajin aikin gama gari, domin bayyana ɓacin rai, ga matakin da gwamnati ta ɗauka na yin kwaskwarima ga biyan kuɗaɗen fensho. Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Halima Balaraba Abbas