Zanga-zanga a Faransa. | Labarai | DW | 04.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Faransa.

An yi zanga-zangar kare haƙkin 'yan ƙabilar Roma a Faransa.

default

'Yan zanga-zangar nuna adawa da korar 'yan Roma a Faransa.

Ƙungiyoyin ƙwadago da na kare haƙƙoƙin bani adama sun shirya wata gagarumar zanga- zanga a ƙasar Faransa, domin nuna adawa ga abin da su ka kira wuce gona da iri da shugaban ƙasa, Nikola Sarkozy ke yi, ta fannin matakan tsaro.Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai ga matakin da gwamnatin Faransa ta ɗauka, wajen korar Romawa ´yan kaka gida, zuwa ƙasashensu na asali, mussamman Rumaniya da Bulgariya. A ɗaya wajen, sun ƙalubalanci dokar da ta tanadi ƙwace takardar zama cikkaken ɗan ƙasar Faransa, ga mutumen da aka samu da lefin kai hari ga jami'an tsaro.

Ranar Talata mai zuwa idan Allah ya kai mu, Sarkozy zai fuskanci wani sabon ƙalubale daga ƙungiyoyin ƙwadago, wanda su ka ƙuduri shiga yajin aikin gama gari, domin bayyana ɓacin rai, ga matakin da gwamnati ta ɗauka na yin kwaskwarima ga biyan kuɗaɗen fansho.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Halima Balaraba Abbas