Zanga-zanga a Faransa ta yi ƙamari | Labarai | DW | 29.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Faransa ta yi ƙamari

An sha mummunar artabu a wasu garuruwa na Faransa tsakanin masu zanga-zanga 'yan ƙwadago wanda aka ƙiesta yawansu cewar ya kai mutum dubu ɗari da saba'in da suka bazu a kan tituna da kuma 'yan sanda.

Masu yin gangamin sun cina wuta a wurare da dama tare da ƙone motoci a biranen Paris da Nantes da Rennes da kuma wasu sauran yankunan.'Yan sanda sun cafke mutane kusan 124 yayin da wasu sama da 50 sun jikkata a ciki har da 'yan sanda 24.Ministan cikin gida na Faransa Bernard Gazeneuve ya yi tsokaci a kan lamarin.

''Ina yin Allah wadai da babbar murya a game da wannan ta'adi na farfasa gine-gine da ƙone ƙone da masu yin gangami suka yi.''Watannin biyu ke nan da suka wuce da ma'aikata da ƙungiyoyin suke yin zanga-zanga a Faransar a kan dokar da gwamnatin ta amince da ita a kan ma'aikata wadda 'yan ƙwadagon ke cewar tana nuna fifiko ga waɗanda suka mallaki kamfanoni da masana'antu.