Zanga-zanga a Faransa ta ɗauki saban sallo | Labarai | DW | 20.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Faransa ta ɗauki saban sallo

A ƙalla mutane dubu ɗari bakwai, a cewar haɗin gwiwar ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar Faransa, su ka fito a titina, domin shirya zanga -zangar nuna adawa ga matakin da gawmnatin ƙasar ta ɗauka, na rage yawan ma´aikata, da kuma matsalolin rayuwa da su ke fuskanta, a sakamakon ƙarancin albashi.

A wani mataki na ba zata, jami´an tsaro, sun bada haɗin kai ga masu zanga-zangar, inda suma suke ƙorafi da matsalolin rayuwa.

Saidai ya zuwa yanzu, shugaban ƙasar Faransa Nikolas Sarkozy na nuna halayen ko in kulla, ga wannan zanga-zanga.