Zanga-zanga a birnin Zagreb don yin tir da kame Janar Gotovina | Labarai | DW | 09.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a birnin Zagreb don yin tir da kame Janar Gotovina

Daruruwan mutane a Zagreb babban birnin Kuratiya sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da cafke tsohon janar din kasar Ante Gotovina. Masu zanga-zangar sun zargi FM Ivo Sanader da cin amanar tsohon janar din wanda ya ke daya daga cikin tsofaffin hafsoshin sojin tsohuwar tarayyar Yugoslabiya da ake nema ruwa a jallo. A ranar laraba da ta wuce aka kame janar Gotovina a tsibrin Teneriffa dake kasar Spain. Yanzu haka dai hukumomin Spain sun amince su mika shi ga kotun duniya dake birnin The Hague wadda ta tuhume shi da aikata laifukan yaki da suka hada da kisan gilla da tilastawa mutane tashi daga yankunan su na asali a lokacin yakin yankin Balkan a cikin shekarun 1990.