1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zanga a birnin washinton na kasar Amurka

November 15, 2005
https://p.dw.com/p/BvKz

Dubbannin yan kasar habasha ne a yau suka gudanar da wata zanga zanga a tsakiyar birnin Washinton na kasar Amurka, don nuna adawar su game da yadda gwamnatin Amurka ke bawa Faraminista Meles Zenewi goyon baya, duk kuwa da asarar rayuka da aka fuskanta game da yamutsin harkokin siyasa a kasar.

A cewar wadanda suka shirya wannan zanga zanga, akwai yan kasar ta habasha a kalla dubu ashirin daga jihohin Amurka da kuma kasar Kanada da suka hallarci wannan zanga zanga.

A cewar Mr Bekalu Ayalew, na jam´´iyyar juyin juya hali ta kasar, dake da hadin gwiwa da wasu kungiyoyi na yan kasar mazauna Amurka,cewa yayi makasudin wannan taro shine a janyo hankalin mahukuntan na Amurka daina bawa gwamnatin ta habasha goyon baya bisa hujjar cewa gwamnati ce ta

Kasar dai ta Habasha ta fada rikicin na siyasa ne a sakamakon zabubbuka na yan majalisun dokoki da aka gudanbar,wanda jamiyyun adawar kasar suka ce an tafka magudi a cikin sa.

Rikice rikicen da kasar ta fuskanta da kuma irin rikon sakainai kashin da yan sanda suka yi ya haifar da asarar rayuka a 83, ban da wasu da dama da suka jikkata.