Zanga Zanga a birnin Bissau | Siyasa | DW | 23.05.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga Zanga a birnin Bissau

Rikicin siyasa na cigaba da addaban Guinea Bissau dake yammacin Afrika mai alumma million1.5

default

A jiya ne dubban magoya bayan hambararren shugaban kasar Guinea Bissau Kunba yalla suka gudanar da zanga zangar nuna bacin ransu dangane da kawara shugaban riko Henrique Rosa waadin cigaba da jan karagar mulkin kasar.

Zanga zangar data gudana a birnin Bissau dake kasancewa fadar gwammnati ,na kira ga gwamnatin shugaba Rosa datayi murabus,koda yake basu samu daman kewaya dukkan fadar kassar ba saboda jamiaan tsaro da aka watsa kotaina dauke da bindigogi da gurneti da barkonon tsohuwa.

Tun a shekarata 2003 nedai aka kifar da gwamnatin Kumba Yalla,amma a makon daya gabata ya sanar dacewa har yanzu shine shugaban wannan karamin kasa dake yammacin Afrika,batu kuma da ake ganin cewa zai iya barazana wa shirin gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 19 ga watan yuni idan mai duka ya kaimu.

Daman dai a wannan wata ne aka shirya gudanar da zabe a Guinea Bissau data kasance a karkashin mulkin mallaka na Potugal,domin maido da gwamnatin democradiyya,Amma gawamantin rikon kwarya a karkashin jagorancin Rosa,ta dage wannan zabe zuwa watan gobe,jinkirin da jamiai danganta da rashin kammala shirya kayyayakin aiki.

A dangane da hakane jammiyar tsohon shugaba Kumba Yalla PRS tace jammiyyun adawa basu amince da dage wannan zabe ba,abunda ke nufin cewa waadin gwamnatin shugaba Rosa na yanzu ya kare kana kasancewarsa kann mulki ya sabawa kaida.

Sakataren jammiyar PRS Antonio Artur Sanha ya bayyana taron magoya bayan tshohon shugaban dake zanga zanga cewa,akwai babban gibi a harkokin siyasar Guinea Bissa,wanda ya kamata ya samu sabon shugaban kasa tun ranar 7 ga wannan wata da muke ciki.

Masu koken dai sun hallara ne a yankin Lala Quema dake birnin Bissau,inda kuma tsohon shugaban keda magoya baya da dama,anan ne suka sanar da dakatar da machin da suka shirya gudanarwa sassa daban daban cikin wannan birni.

Mr Sanha ya fadawa taron manema labaru cewa sun dakatar da wannan machi ne saboda jamiaan tsaron sun dfauki alkawarin bindige masu zanga zangar.To sai dai babu tabbaci dangane da wannan furuci nasa.

A daidai lokacin da ake shirin gudanar da wannan zanga zanga nedai tsohon shugaba Yalla ya samu gayyata daga shugaba Abdoulaye Wade na Senegal dake makwabtaka,wanda ke zama daya daga shugabannin kasashe uku na yankin dake shiga tsakani wajen warware wannan rikici na Guinea Bissau tun barkewansa.

Wani Babban jammiin gwamnati daya samu halartan ganawar tasu ya bayyana cewa shugaba Wade na Senegal yayi kira ga Yalla da ya sake laakari da bayyana kansa da yayi a matsayin shugaban kasa a makon daya gabata.

To sai dai a nashi bangaren tsohon Shugaban na Guinea Bissau yayi nuni dacewa bazai iya zartar da hukunci a take ba ,yana bukatar lokaci na tuntubar mataimakansa.

Yalla wanda da farko ya samu karbuwa tsakanin matasa marasa aikin yi dake biranen kasar ,yace yayi murabus daga mulki ne bisa tilastawa.

Tun a ranar asabar nedai shugaba Wade na senegal da shugaba Olusegun Obasanjo na Nigeria kuma jagoran kungiyar gamayyar Afrika da shugaba Tanja Mammadou shugaban kasar Niger da kungiyar cinikayya ta Ecowas suka suka kai gajeriyar ziyara a Guinea Bissau domin tattauna wannan rikici.

A
 • Kwanan wata 23.05.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvbk
 • Kwanan wata 23.05.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvbk