Zanga zanga a birnin Benghazi na kasar Lybia ta hadasa mutuwar mutane | Labarai | DW | 18.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zanga a birnin Benghazi na kasar Lybia ta hadasa mutuwar mutane

A ci gaba da zanga zangar da kasashen musulmi ke yi, bayan zanen batanci da wata jaridar Danemark ,ta yi, na hoton Manzan Allah, tsira da amincin Allah su tabata a gare shi,a kasar Lybia, an yi arangama tsakanin jami´an tsaro, da masu zanga zanga, da su ka kai hari, ga karamin opishin jikadancin kasar Italia dake Benghazi.

A sakamon wannan arangama, mutane kussan 20 su ka rasa rayuka, a cikin harbe harben, kan mai uwa da wabi, da jami´an tsaro su ka yi, domin tarwatsa masu zanga zangar.

Al´umma kasar Lybia ta shirya wannan zanga zanga a opishin jikadancin Italia, domin maida martani ga ministan sake passalin dokokin kasar Italia, da ya buga riguna dauke da hoton zanen batancin,abinda musulmi ke dauka tamkar karin wulakanci ga Annabin rahama.

Hukumomi kasar Lybia, sun hiddo sanarwa, a game da wannan zanga zanga, sun kalubalanci wanda su ka shiraya ta, tare kuma da yin Allah wadai, ga zanen batancin, da duk wani abun da zai sabawa addini.