Zanga zanga a Abidjam | Labarai | DW | 19.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zanga a Abidjam

Daruruwan magoya bayan shugaba Lauren Gbagbo na kasar Ivory Coast ne ke gudanar da bore a manyan titunan birnin Abidjam,domin bayyana adawansu da shirin takardar shaidan dan kasa,da aka kaddamar gabannin zaben watan Oktoba.

Kungun matasan dake marawa shugaban kasa baya sun dakatar da harkokin sufuri a Abidjam din dake zama cibiyar kasuwancin kasar,inda suke kone konen tayoyi,tare da jifan wasu masu ababan hawa da ke kokarin wuce wuraren da suka sa shinge.

Rahotanni daga wasu unguwannin na Abidjam kuwa na nuni dacewa an samu tashe tashen hankula a tsakanin maaikata,ayayinda sauran harkokin kasuwanci suka tsaya cik sakamakon wannan zanga zanga da matasan ke gudanarwa.

Magoya bayan Shugaba Gbagbo dai sun lashi takobin dakatar da shirin takardun shaidan yan kasa da ake gudanarwa a Ivory coast din,adangane zargin cewa yan adawa na iya amfani da shirin wajen samarwa miliyoyin baki takadun da zai basu daman shiga zabe.