Zanga zanga a ƙasar Togo | Siyasa | DW | 13.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga zanga a ƙasar Togo

Ana zanga zagar lumana kashi biyu a ƙasar Togo, tsakanin 'yan adawa da magoya bayan gwamnati

default

Masu zanga zanga a Togo

Ana gudanar da zanga zangar lumana kashi biyu a ƙasar Togo. Rohotanni suka ce magoya bayan madugun 'yan adawa Jean Pierre Fabre na jam'iyar UFC, suna ta su zanga zangar a wajen helkwatar jam'iyarsa sanye da riguna masu launin ruwan ɗorawa, a yayin da magoya bayan gwamnati suke ta su zanga zangar a tsakiyar birnin na Lome sanye da fararen riguna. Jam'iyar adawa ta UFC a ƙasar ta Togo, ta shirya gudanar da wata sabuwar zanga zanga, domin nuna damuwa akan sake zaɓen da aka yi wa Faure Gnassinbe Eyadema a matsayin shugaban ƙasa, zaɓen da 'yan adawa suka ce ya na cike da maguɗi. Kanfanin dillanci labarai na AFP ya ambato jagoran 'yan adawar Jean Pierre Fabre ya na cewa za su nunawa Faure Gnassinbe sune ke da jama'a kuma ta kowane hali za su ƙubutar da ƙasar ta Togo daga mulkin kama karya. Muhukunta suka ce an raba hanyar da masu zanga zangar dake adawa da juna ke bi. A ranar Talatar da ta gabata 'yan adawan ƙasar sun so su yi zanga zanga to  amma ba su samu izini daga hukumomin ba, abin da ya sa aka tarwatsa su a lokacin da suka taru domin yin jerin gwano. Masu aiko da rahotanni sun ce wasu majiyoyin daga gwamnatin suka ce izuwa yanzu dai ba wani ƙudurin doka da ta haramta zanga zangar ta yau. Faure Eyadema dai ya hau mulkin ƙasar a shekara ta 2005 bayan da babansa janaral Gnassinbe Eyadema ya mutu, bayan shekaru kimanin arba'in yana mulkin ƙasar shi kaɗai.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita Mohammad Nasiru Awal