Zanga-zanga a ƙasar Masar | Labarai | DW | 21.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a ƙasar Masar

A ƙasar Masar masu adawa da batun ɗan Hosni Mubarak ya ya gaji kujerar baban a shugabancin ƙasar sunyi dafifi a fadar shugaban ƙasar.

default

Jamal Mubarak, da babansa Hosni Mubarak

Daruruwan mutane a ƙasar Masar, sun gudanar da zanga-zanga a birnin Alƙahira, domin nuna adawarsu kan raɗe raɗin da ake yi cewa ɗan shugaba Hosni Mubarak ne zai gaji kujerar shugaban ƙasar, wanda ma haifinsa ke kai.

Masu zanga-zangar da suka yi cincirindo a ƙofar gidan shugaban ƙasar sun ce su basa son gwamnatin gado ba kuma sa son a ɗora musu Gamal, wato ɗan shugaba Hosni Mubarak.

An dai girke 'yan sanda da yawa a wuri zanga zangar da ta haɗa magoya bayan babbar jam'iyyar adawa ta ƙasar wato Kefaya movement da kuma wakilan sauran jam'iyyun adawar ƙasar

Mawallafiya: Halima Umar Sani

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal