Zanga zanga a ƙasar Hungary | Labarai | DW | 24.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zanga a ƙasar Hungary

Mummunan zanga zangar adawa da gwamnati a kasar Hungary ya dabaibaye shagulgulan bikin zagayowar cika shekaru 50 nuna adawa da tarayyar Soviet. Yan sandan kwantar da tarzoma sun shafe tsawon daren jiya har ya zuwa safiyar yau Talata suna fafatawa domin tarwatsa masu zanga zangar inda suka rika harbi da harsasan roba tare da yin feshin ruwan zafi. A kalla mutane kusan dari daya ne suka sami raunuka, yayin da yan sanda suka yi awon gaba da wasu mutum 40. Wakilai daga kasashe kimanin 50 suka hallara a kofar majalisar dokokin Hungary inda aka gudanar da bikin tunawa da boren na 1956. Shugaban kasar Jamus Horst Köhler na daga cikin wadanda suka halarci bikin. Boren na 1956 ya samo asali bayan da dalibai suka gudanar da zanga zangar adawa da gwamnatin kwaminisanci ta tarayyar Soviet abinda ya yi sanadiyar mutuwar yan kasar Hungarin kimanin 2,800, wasu 12,000 kuma suka sami raunuka. Tun daga wannan lokaci ne a duk shekara ake gudanar da bikin zagayowar ranar domin nuna alhini ga wadanda suka rasa rayukan su.