Zanga-zanga a ƙasar Masar
September 21, 2010Talla
Daruruwan mutane a ƙasar Masar, sun gudanar da zanga-zanga a birnin Alƙahira, domin nuna adawarsu kan raɗe raɗin da ake yi cewa ɗan shugaba Hosni Mubarak ne zai gaji kujerar shugaban ƙasar, wanda ma haifinsa ke kai.
Masu zanga-zangar da suka yi cincirindo a ƙofar gidan shugaban ƙasar sun ce su basa son gwamnatin gado ba kuma sa son a ɗora musu Gamal, wato ɗan shugaba Hosni Mubarak.
An dai girke 'yan sanda da yawa a wuri zanga zangar da ta haɗa magoya bayan babbar jam'iyyar adawa ta ƙasar wato Kefaya movement da kuma wakilan sauran jam'iyyun adawar ƙasar
Mawallafiya: Halima Umar Sani
Edita: Ahmadu Tijjani Lawal