1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a ƙasar Hongrie

September 19, 2006
https://p.dw.com/p/Buj1

Praministan ƙasar Hongrie, Ferenc Gyurcsany, ya yi tsaye kan bakan sa, na ƙin sauka daga mukamin sa,duk da zanga zangar da al´ummar ƙasar ke yi ta cimma wannan buri.

A sahiyar yau ma, dubunan jama´a, sun taru, a harabar majalisar dokoki da ke Budapest, babban birnin ƙasar, inda su ka shiga zaman durshin, na sai Praminsitan da su ka kira maƙaryaci, yayi murabus.

Wannan zanga zanga, ta samu asuli daga wani jawabin sirri, da gidan Redio na ƙasa ya watsa, wanda a cikin sa,Frenec Gyurcsany, ya hurta cewa, zai ɗauki tsauraran matakai na ƙuntatawa jama´a, da zaran a ka zaɓe shi, wannan jawabi ,ya saɓawa alƙawuran da yayi, a lokacin yaƙin neman zaɓe, na watan Aprul da ya cuce.

Masu zanga zangar, na zargin sa da yaudara jama´a, ta hanyar shirga masu ƙarya.

A daren jiya, dubunan masu jama´a, sun yi kwanan zaune, a gidan Talbajan na ƙasa da su ka mamaye.

Ya zuwa yanzu, jam´ian tsaro na ci gaba da yunƙurin tarwatsa su, a sakamakon arangamar da a ka tabka, mutane kussan 200 su ka ji raunuka.