1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zanga a ƙasar France

March 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4g

A ƙasar France, zanga zangar da a ka gudanar, ta sha ban bam da sauran ƙasashen turai.

A ƙalla mutane million ɗaya, mussamn matasa yan makaranta,da ƙungiyoyin ƙwadago, a birane daban daban, na ƙasar sun ka shirya tafiyar jerin gwano, don nuna adawa, ga wata sabuwar doka,da gwamnati ta ƙaddamar, a game da ɗaukar ma´aikata.

Wannan doka mai suna CPE, wato Conrtat Premiere Ambauche, da ake ta kai ruwa rana a kanta, a France, ta tanadi cewar, shugabanin kampanoni, na da yancin ɗaukar sabin ma´aikata a maddadin gwaji ,har tsawan shekaru 2, idan kuma, basu da buƙatar ci gaba, da aiki tare su, za su iya sallamar su a take, a ƙarshen wannan wa´adi.

Gwamnati a cewar Praminista, Dominique De Villepin, ta ɗauki wannan mataki, domin samar da ayyukan yi, ga matasa wa´anda a halin yanzu ke fama da zaman kashe wando.

A nasu ɓangare yan makaranta, sun yi alƙawarin ci gaba da kokowa, har sai sun ga abinda ya turewa buzu naɗi.