1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zanga a ƙasar Faransa

August 28, 2010

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama na ƙasar Faransa na ƙara matsa ƙaimi ga ƙasar Iran

https://p.dw.com/p/OyZc
Sakineh Mohammadi AsthianiHoto: AP

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bi adama a ƙasar Faransa sun gudanar da zanga zangar nuna goyon baya ga Sakineh Mohammadi Ashtiani wata 'yar ƙasar Iran da ke fuskantar  hukuncin kisa ta hanyar jefewa , bayan da aka sameta da laifin yin zina da kuma bada haɗin kai wajan aikata kisa akan mai gidanta

Zanga zangar wacce ta samu hallarta kimani mutane 300 a birnin Paris na ƙasar ta Faransa masu aiko da rahotanin  sun ce haka kuma  an gudanar da irinta a cikin wasu garuruwa guda 100 na duniya a lokaci ɗaya.

Sakineh Ashtiani mai shekaru 43 da haifuwa an yanke mata hukuncin rajamu ne tun a shekara ta 2006 ,to amma daga bisanin hukumomin na ƙasar ta  Iran sun bada sanarwa ɗage hukumci kafin yanke shawara ta ƙarshe.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita      : Abdullahi Tanko Bala