1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

zanga zamgar tsadar rayuwa a Niger

Zainab A MohammedJune 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6U

Harkokin kasuwanci sun kusan tsayawa cik a birnin yamai fadar gwamnatin janhuriyar niger,sakamakon zanga zangar tsadar rayuwa da kungiyoyin jammaa ke gudanarwa a wannan kasa.Ayayinda bankuna da kamfanonin insura da manyan masanaantu ke gudanar da ayyukansu,yawancin kantuna da cibiyoyin ciniki na rufe,haka zalika marantu da asibitoci,saboda tun a jiya ne maaikata suka fara yajin aiki.

Mazaunan birnin yamai din dai sun sanar dacewa babu motocin daukan pasinja a hanya,kana kasuwannin baki daya na rufe.

Shugaban hukumar yaki da tsadar rayuwa a Niger ,Nuhu Arzika ,tun a jiya ne yayi kira da a gudanar da wannan bore na lumana ,adangane da wahalhalu na rayuwa da talakawa ke cigaba da kasancewa ciki.

Idan baa mance ba,a makon daya gabatane sama da mutane 2,000 sukayi jerin gwano a titunan yamai ,domin bayyana bakin cikinsu dangane matsaloli na tsadar rayuwa a janhuriyar ta Niger.