1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zambiya ta kori jakadan kasar Kuba

Salissou Boukari
April 1, 2018

Shugaban Zambiya Edgar Lungu ya nemi kasar Kuba ta janye jakadanta a kasar ta zambiya Nelson Pages Vilas, wanda zambiyar ke zargi da nuna goyon baya ga wata sabuwar jam'iyyar adawar a kasar.

https://p.dw.com/p/2vLn3
FALSCHE BESCHREIBUNG - Sambia Lusaka Wahlen Präsident Edgar Lungu bei Stimmabgabe
Hoto: Getty Images/AFP/G. Guercia

Shi dai Vilas jakadan kasar ta Kuba a Zambiya, ya halarci bikin kaddamar da sabuwar jam'iyyar ne ta adawa a ranar Asabar a Lusaka babban birnin kasar, inda kuma ake zarginsa da furta kalamai a bainar jama'a na goyon bayan wannan sabuwar jam'iyya.

Shugaba Lungu ya nemi da kasar Kuba ta janye wannan jakada nata ta sabili da halaye da ya nuna a cewarsa da suka sha bambam da na jami'in diflomasiyya kamar yadda mai magana da yawun fadar shugaban kasar ta Zambiya ya sanar a gaban manema labarai a ranar Lahadi.