Zambia tace ta komawa China domin samun rance. | Labarai | DW | 11.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zambia tace ta komawa China domin samun rance.

Shugaba Rupia Banda na Zambia ya juya ga China domin samun tallafin kuɗi.

default

Ginin asusun IMF a birnin Washington na Amirka.

Shugaba Rupia Banda na ƙasar Zambia ya bayyana cewar, ƙasarsa ta mayar da hankali ga ƙasar China domin samun tallafin kuɗi bisa la'akari da irin ƙarancin kuɗin ruwar da China ɗin ke karɓa. Shugaban na Zambia, wanda ke karɓar baƙuncin babban darektan asusun bayar da lamuni a duniya na IMF Dominique Strauss - Kahn, ya shaidawa baƙon nasa cewar, sauƙin kuɗin ruwar, na daga cikin dalilan da suka sa Zambia karkata ga China domin samun rance. Banda, ya ƙara da cewar, tattalin arziƙin Zambia ya sami bunƙasa a dai dai lokacin da ƙasashen duniya daban daban suka fuskanci matsalar koma baya, inda ya ce, ta yi nasarar cimma hakanne saboda kyawawan manufofin tattalin arziƙin da gwamnati ke yin amfani dasu. A makon jiya ne dai, Shugaba Rupia Banda ya kammala ziyararsa ta yini goma a ƙasar China, inda ya dawo gida da rancen kuɗi na dala miliyan dubu ɗaya, bayan da ƙasashen biyu suka sanya hannu akan yarjeniyoyin tattalin arziƙi daban daban. Zambia na samun kashi 80 cikin 100 na kuɗin shigarta ne daga ma'adinin Tagulla.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh.

Edita: Muhammad Nasir Awal.