Zamantakewa tsakanin musulmi da kristoci a jamus | Zamantakewa | DW | 22.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Zamantakewa tsakanin musulmi da kristoci a jamus

Zaman lafiya madogarar cigaba

Wolfgang Schäuble

Wolfgang Schäuble

“A kwai kimanin alummomin musulmi sama da million uku dake da zama a nan tarayyar Jamus,kuma musulumci ya kasance bangare na rayuwarmu baki daya,kana yanda matukar muhimmanci mu gudanar da zamantakewarmu da juna ta hanyar da zamu fahin musulmi,kuma suma a bangaren musulmin hakan ya zamanto wajibi”.

Wadannan sune kalamun ministan kula da alamura na cikin gida na nan tarayyar jamus Wolfgang Schäuble, a wata hira da jaridar gabashin kasar dake fitowa a kowace rana tayi dashi.kuma wannan zamantakewa na cudeni in cudeka tsakanin mabiya addinai daban daban dake zama anan jamus shine batu da shirin taba ka lashe na wannan makon zaiyi nazari akai.

Kamar kowace kasa ta turai tarayyar jamus kasace dake da dumbin musulmi da ke zaune acikin,wadanda mafi yawansu kuwa baki ne da suka fito daga kasashe daban daban na duniya, ayayinda a hannu guda kuma akwai musulmi jamusawa da dama,inda kuma a kullum dada samun karuwan jamusawa akeyi wadanda suke musulunta.

Kasancewa a kulllun zaman lafiya shine madogara na cigaban kowace alumma a kowane yanayi na rayuwa,hukumomin kasar ta jamus sun duka kain da nain wajen ganin cewa an samu fahintar juna tsakanin magoya bayanan addinai daban daban dake kasar.

Ministan kula da harkokin cikin gida na nan kasar Wolfgang Schäuble,ya jaddada bukatar musumi da christoci su rika zama teburin mahawara domin tattauna batutuwa da suka shafi zamantakewa na yau da kulum tsakaninsu.Dalili kenan daya sanya a halin yanzu aka sanya harkoki na na rayuwar addinin Islama cikin batutuwa na zamantakewan alummomi na jamus baki daya,Inji Schäuble

Wolfgang

“Idan musulmin suna da zama ne a anan jamus,sukan hayayyafa ne fiye da yadda iyaye christoci ke haihuwa,shine dole mutun ya tambaya, ta yaya a kullum muke neman zarginsu?ayayinda a hannu guda kuma iyaye cchristoci daga dariku daban daban keda yara kalilan?Ko kuma idan aka mutum yana yawan zuwa masallaci ,me yasa muke yawan zarginsa?ko kuma idan ya kasance musulmi na tafiya masallaci a kowace jumaa,kuma mu bama yawaita zuwa churci a kowace ranar lahadi?Kuma a hakan babu wanda ke dauke da alhakin wani”

Ministan harkokin cikin gidan yace a wasu lokutan akan samu kura kurai a bangarensu,ayayinda suka san ya zamanto wajibi wa mafi yawan alummomin dake zaune a kasannan wadanda christoci ne,bayan aure na shekara guda sukan nemi takadar izinin kasa da sunan iyali,hakan ya zamanto a bu mawuyaci a bangaren musulmai dake da zama a wannan kasar,inji dan jamiiyyar ta christian Demokrat

“Idan mutane suna da yara kalilan,wani lokaci nan gaba suna iya fuskantar matsaloli a makomar rayuwarsu nan gaba.Adangane da hakane yake da muhimmanci a hada kai ,tare da dogaro da juna.Kuma dole ne mu bayyana cewa ,muma a namu bangaren muna da na mu laifi.Amma da taimakon ku agaremu,zamu iya samarda zaman lafiya da kwanciyar hankali wa musulmi,ko kuma akasin haka”

Ministan harkokin cikin gidan kuma dan jammiyar CDU dai,ya jaddada bukatar darajawa aladu da rika bin kaidoji da addinai suka gindaya Ta hakan ne inji Mr schäuble sauran jamaa zasu iya yin koyi da dokoki da ma yanayin yadda addinin musulunci ya tsara rayuwar mutane.

Wata matsala da har yanzu take kawo cikas cikin wannan kokari da akeyi na inganta zamantakewa tsakanin mabiya addinai anan tarayyar jamus dai,shine manufar yancin walwalka na tafiyar da harkokin addini,kamar yadda yake kunshe cikin dokar kasa,wanda kuma zaa iya cewa ya taallaka ne da tsarin darikokin church dake kasar,inji Mr Schäuble dake zama dan darikar protestant.

Adangane da hakane ya nanata bukatar kowa ya darajawa addinin wani ,domin akwai ababai na rayuwa da zaa iyayin koyi daga juna,wadanda kuma zaa iya cin moriyarsu a rayuwa.

“Idan baa bukatar fahintar juna,dalili menene yasa ake zamantakewa tare,da kuma bukatar zama wuri guda da juna?Kuma anayin haka ne ba tare da laakari da banbancin addini ba,daga farko har zuwa karshe.Kuma akan wannan tafarki ne mutane ke gudanar da rayuwarsu.”

Ministan harkokin cikin gidan na jamus ya jaddada cewa babu abunda ya hada koyin addinin musulunci da harkoki na tarzoma kamar yadda duniya takewa addinin hange daga nesa.Yace tsattsauran raayi na addini nada manufofi daban daban.Schauble yace fahintar juna tsakanin mabiya addinai daban daban musamman musumi da christoci yanada matukar muhimman,a zamantakewa na makwabtaka,domin hausawa nacewa makwabcinka danuwanka.