Zaman zullumi a Cote d'Ivoire
November 26, 2010Tun kwaniki da Zaɓen ke kusatowa, zaman zullumi ya ƙaru matuƙa a ƙasar ta Cote d'Ivoire
, gabanin zaɓen zagaye na biyu da za'a yi jibi Lahdi. Zaɓen shine ake fatan ya kawo ƙarshen rashin jituwa da aka yi fama da shi, tun shekaru takwas da suka gabata, bayan da aka gwabza yaƙin basasa, abinda ya kai ga raba ƙasar gida biyu, kafin a samu sasantawar da ta kowa ƙwarya-kwaryan kwanciyar hankali a ƙasar dake yammacin Afirka. An dai samu tashin-tashina nan da can, tun a zaɓen shugaba ƙasar zagayen farko wanda aka yi a watan jiya, inda shugaba mai ci Lauren Gbagbo da tsohon Firimiyan ƙasar kuma wanda ya taɓa kasancewa babban jami'i a bankin duniya wato Alhassan Ouattara. A zaɓen na farko dai 'yan takaran biyu sunyi kan kankan, don haka yanzu za su shiga zagaye na biyu a jibi lahdi, da yardan mai duka.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu