1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman makokin marigayi tsohon Sultan Dasuki

November 16, 2016

A ranar Talata 15.112016, aka yi jana'izar marigayi tsohon sarkin Musulmi na 18 a Najeriya Alhaji Ibrahim Dasuki a garin Sakkwato, wanda ya bar duniya ya na da shekaru 93 a duniya.

https://p.dw.com/p/2SmP3
Nigeria Sultanspalast in Sokoto
Hoto: DW/T. Mösch

Ya rike sarautar Baraden Sakkwato, matsayin da ya yi amfani da shi wajen gudunmawar kafa kungiyar Jama'atul Nasril Islam, kafin ya zama sarkin Musulmi a shekara ta 1988. Ya kasance sarkin Musulmi na farko daga zuri'ar Buhari dan Sheikh Usman bin Fodiyo.

Marigayin ya zama Sarkin Musulmi a watan Disambar shekara ta 1988 bayan rasuwar Sarkin Musulmi na 17 Alhaji Abubakar Sadik na III. Sanar da shi a matsayin magajin Sarki Abubakar na III a maimakon dansa Alhaji Muhammadu Maccido Abubakar III ya jawo wata zanga-zanga ta tsawon kwanaki biyar a birnin na Sakkwato wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 10

Ya kwashe shekaru takwas kan mulki kafin gwamnatin soji ta Marigayi Janar Sani Abacha ta sauke shi a shekara ta 1996. Mai shekaru 93 a duniya, Alhaji Ibrahim Dasuki wanda shi ne mahaifin tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan al'amuran tsaro, Kanar Sambo Dasuki ya rasu ya bar 'ya'ya da jikoki masu yawa, ciki kuwa har da shi Kanar Sambo Dasukin.