1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman majalisar kare hakkin jamaa ta MDD akan darfur

December 13, 2006
https://p.dw.com/p/BuY4

Ayau ne majalisar kare hakkin biladama ta mdd zata koma teburin tattaunawa adangane da rikicin lardin darfur din kasar >Sudan,batu daya kawo rarrabuwar kawuna tsakanin kasashe membobi duk da kira da sakatare general na majalisar Kofi Annan ,na bukatar hadin kai da zartarwar gaggawa tsakaninsu kann wannan batu.A jiya nedai aka aka shirya kada kuriu dangane da sake tura ayayrin jamian gani da ido a wannan yanki dake fama da rikici a yammacin Sudan.To sai dai baa samu cimma daidaito tsakanin wakilan kasashe na yammaci da takwarorinsu na Afrika dana sauran kasashen musulmi ba.A wani abunda ke zaba dada rinchabewar lamura a kann lardin na Dafur,Premier Tony Blair na Britania ya marawa ,kudurin Amurka baya,adangane da aiwatar takunkumin bin sararin samaniyan yankin.Mr Annan dai ya jaddada cewa yana da matukar muhimmanci wakilan kasashe 47 dake majalisar cimma matsaya guda adangane da tura tawagar jamian gani da ido zuwa Darfur.