1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman majalisar dokokin Isra´ila Knesset

April 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1k

A yau sabuwar majalisar dokokin Isra´ila zata fara zaman ta na farko, inda FM rikon kwarya Ehud Olmaert zai kammala tattaunawar kafa wata sabuwar gwamnatin kawance. Tsohon FM Shimon Peres zai jagoranci zaman majalisar a matsayinsa na dan jam´iyar FM Olmert wato Kadima. Shi ma shugaba Moshe Katsav zai halarci zaman majalisar ta Knesset. Jam´iyar Kadima ta lashe kujeru 29 daga cikin 120 na majalisar dokokin a babban zaben da ya gudana a ranar 28 ga watan maris.