Zaman mahawarar majalisar dokokin Jamus ta Bundestag akan rikicin Sudan | Siyasa | DW | 27.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaman mahawarar majalisar dokokin Jamus ta Bundestag akan rikicin Sudan

A zaman mahawarar da ta yi domin bitar rikicin kasar Sudan, a jiya laraba, majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta amince da takardar shawarar da gwamnatin hadin guiwa ta SPD da The greens ta gabatar domin yin kiran ba da kafar kai taimakon jinkai ga mutanen da suka tagayyara a Darfur da kuma neman MDD da ta kakaba wa fadar mulki ta Khartoum takunkumin cinikin makamai

Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag

Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag

Ko da yake sakatare-janar na kungiyar taimakon jinkai ta Jamus Welthungerhilfe ya bayyana tababa, amma akalla kungiyar tasa ta samu tambarin fadar mulki ta Khartoum a game da izinin kai taimako ga mutanen da suka tagayyara a lardin Darfur dake fama da yakin basasa a yammacin kasar Sudan. Tun a cikin watan afrilun da ya wuce ne kungiyar ta tura kayan taimako zuwa Khartoum a cewar sakatare-janar dinta Hans-Joachim Preuß, wanda ya kara da bayani yana mai cewar:

Kimanin tan dubu da dari na kayan abinci muka dirke a garin Khartoum kuma tuni wani bangare ya isa ga mabukata ko da yake ba a tabbatar da hakan a hukumance ba. Kuma tun daga ranar daya ga watan yuni mai kamawa za a yi jigilar hatsi na tan dubu 14 zuwa yankin.

A hadin guiwa da kungiyar taimakon abinci ta MDD kungiyar ta Welthungerhilfe ke fatan daukar matakai na kandagarkin wata masifar da aka fara hangen alamomin afkuwarta a yankin Darfur dake yammacin Sudan, musamman ma dangane da karatowar yanayin damina.

A zaman mahawarar da suka yi a jiya laraba, wakilan majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, sun amince da shawarar da jam’iyyun SPD da the Greens suka gabatar, inda suke kira ga gwamnatin Sudan da ta ba wa kungiyoyin taimakon jinkai na kasa da kasa damar kai kayan taimako zuwa Darfur ba da wata-wata ba. Dukkan wakilan majalisar sun bayyana goyan bayansu ga kiran da MDD tayi na cimma zama zaman lafiyar yankin. A shekaran jiya talata ne kwamitin sulhu na MDD ya gabatar da kira ga fadar mulki ta Khartoum da ta cika alkawarin da tayi na kwance damarar makaman dakarunta na sa kai a Darfur. A lokaci guda ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemarie Wieczorek-Zeul ta yi kira ga MDD da ta sanya takunkumin haramta sayarwa da kasar Sudan makamai. Ta ce tuni dai Kungiyar Tarayyar Turai ta kakaba wa Sudan irin wannan takunkumi saboda ta haka ne kawai za a ja kunnenta. Ministar kazalika ta mika godiyarta ga mutanen da suke sadaukar da rayukansu a kokarin kai taimako ga Bayin Allahn dake cikin hali na zautuwa a Sudan. Ministar dai tana da hannu a takardar shawarar da jam’iyyun SPD da the Greens suka zayyana, wacce kuma dukkan wakilan majalisar Bundestag suka amince da ita ba tare da musu ba. Takardar tayi kira ga KTT da ta ba da taimakon kudi domin tallafa wa aikin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Kungiyar Tarayyar Afurka.