Zaman lafiyar kasar Sri Lanka kan sabuwar turba
November 25, 2005Talla
Sabon shugaban Sri Lanka Mahinda Rajapakse ya ce zai ci-gaba da girmama yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da ´yan tawayen Tamil Tigers to amma akan wani sabon sharadi. A jawabin da yayiwa majalisar dokokin kasar shugaban ya ce dole ne a sake gudanar sabbin shawarwari game da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiyar ta shaekara ta 2002. Sabon shugaban ya ce dole ne a sake fasalta yarjejeniyar ta yadda zata haramta daukar kananan yara aikin soji. Tun kimanin shekaru biyu da suke wuce shawarwari wanzar da zaman lafiya stakanin ´yan tawayen Tamil Tigers da gwamnatin Sri Lanka ke tafiyar hawainiya. Kasar Norway ce ke kokarin yin sulhu tsakanin sassan biyu.