Zaman lafiya ya fara wanzuwa a Somalia | Labarai | DW | 23.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman lafiya ya fara wanzuwa a Somalia

Shugaba Abdullahi Yusuf na Somalia, yace a shirye yake ya tattauna da wakilan addinin Islama na kasar, a wani yunkuri na dakile ci gaba da zubar da jini.

Abdullah Yusur ya fadi hakan ne , yayin da yake gabatar da jawabi aci gaba da ziyarar da yake a birnin London.

Bugu da kari, shugaban na Somalia ya kuma shaidar da cewa, duk wata kungiyya da take son shiga wannan tattaunawa ta sulhu to dole ne ta ajiye makaman ta tukuna.

Ya zuwa yanzu dai a cewar Abdullah Yusuf, gwamnatin rikon kwarya ta kasar ce ke rike da madafun ikon tafiyar da al´amurra a kasar.

To amma duk da haka a cewar shugaban na Somalia, za a dauki lokaci kadan kafin tabbatar da ingantuwar doka da oda a fadin kasar baki daya.

Idan dai an iya tunawa a farko farkon wannan makon sai da mutane 12 suka rasa rayukan su a birnin Magadishu, bayan wani dauki ba dadi daya wanzu, a tsakanin dakarun gwamnati da kuma tsagerun kotunan islama na kasar.