1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman lafiya ya fara samuwa a Ivory Coast

January 19, 2006
https://p.dw.com/p/BvBb

Daruruwan matasa dake gudanar da zanga zanga a birnin Abijan na kasar Ivory Coast, sun yi shakulatin bangaro da kiran da Shugaba Lauret Gbagbo yayi musu na daina tada zaune tsaye a kasar.

Bayanai daga birnin, sun nunar da cewa mutane sun fara ci gaba da gudanar da rayuwar su to sai dai ba kamar yadda yake ada ba, domin kuwa har yanzu tsagerun matasan na ci gaba da daddatse manya manyan titunan dake cikin birnin na Abijan.

Matasan , wadanna aka bayyana su da cewa magoya bayan shugaba Lauret Gabgbo ne, na gudanar da zanga zangar ne don bukatar ficewar Mdd daga kasar.

Hakan kuwa ya biyo bayan kiran da masu shiga tsakani suka yi ne daga Mdd na ´´a rushe majalisar dokokin kasar, wanda da yawa daga cikin mambobin ta magoya bayan Shugaba Lauret Gabgbo ne.