1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman kwamitin sulhu akan rahoton binciken kisan Hariri

October 25, 2005
https://p.dw.com/p/BvNr
An bude wani zaman muhawwara a kwamitin sulhu na MDD game da rahoton binciken kisan gillar da aka yiwa tsohon FM Lebanon Rafik Hariri. A lokacin da yake jawabi gaban kwamitin sulhu, babban mai shigar da kara na Jamus kuma wanda ya jagoranci wannan bincike Detlev Mehlis ya yi kira ga Syria da ta ba tawagarsa cikakken hadin kai don a cike abinda ya kira wani gibi game da wadanda suka shirya kuma suka aikata wannan ta´adda. Mehles ya yi wannan jawabi ne kwanaki biyar bayan ba da rahoton binciken wanda ya zargi manyan jami´anleken asirin Syria da kuma Lebanon da hannun a fashewar bam din da yayi sanadiyar mutuwar Hariri da kuma wasu mutane 20 a birnin Beirut a cikin watan fabrairu da ya gabata. Jim kadan gabanin yayi jawabi jakadan Amirka a MDD John Bolton da takwaransa na Faransa Jean-Marc de La Sabliere sun ce zasu nemi goyon bayan wani kudurin da zasu gabatar wanda zai matsawa gwamnatin birnin Damaskus lamba don ta ba da hadin kai.