Zaman juyayi a China | Siyasa | DW | 19.05.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaman juyayi a China

An fara zaman makoki na yini uku a China don juyayin mutanen da girgizar ƙasar nan ta rutsa da su

default

Tutar China a rabin gora

Mako guda bayan mummunar girgizar ƙasar da ta auku a China, a yau litinin aka fara zaman makoki na kwanaki uku don tunawa da waɗanda suka rasu a wannan bala´i daga Indallahi. An sauko da tutoci sannan an soke gudanar duk wasu shirye-shirye da sauran bukukuwa a cikin ƙasar har ƙarshen zaman makokin.


Tun da sanyin safiyar yau sojoji sun yi maci zuwa dandalin zaman lafiya dake birnin Beijing, inda kamar a duk faɗin ƙasar aka sauko da tutar China zuwa rabin gora. Da misalin ƙarfe biyu da rabi agogon China wato daidai lokacin da girgizar ƙasar ta auku kenan a ranar Litinin ta makon jiya, ƙasar ga baki ɗaya ta tsaya cak. An yi shiru sannan an yi ta buga jiniya tsawon mintoci uku wato tsawon lokacin da ƙasa ta girgiza kenan wadda ta halaka mutane kimanin dubu 50. Mutane ne dai sun fita ƙwansu da kwarkwatansu don nuna juyayinsu.


Wasu ´yan ƙasar kenan da suka hallara a dandalin don nuna alhininsu. Suka ce ya kamata mu da muke raye mu yi juyayin waɗanda suka rasa rayukansu musamman a wannan bala´i.


Tutocin Jamus da na ƙungiyar tarayyar Turai dake a gaban ofishin jakadancin Jamus na daga cikin na ofisoshin jakadancin ƙasashen ƙetare da aka fara sauko da su yau da safe. Su ma kamfanonin ƙetare sun nuna zumuncin su ga al´ummomin China. Yanzu haka reshen ƙungiyar agaji ta Red Cross a Jamus ya tura wani asibiti na tafi da gidanka inda yanzu haka aka kwatar da mutane 120 sannan a tsakiyar wannan mako jiragen samansa biyu da wata tawagar likitoci zasu isa yankin da bala´in ya afkama. Kawo yanzu a cikin Chinar kanta an tara kuɗaɗen taimako kimanin euro miliyan 800. Sannan wani shirin telebijin da aka gudanar jiya an tara ƙarin miliyan 150, kamar yadda masu gabatar da shirin suka nunar.


Atmo TV:


Dukkan ɓangarori na al´ummar ƙasar sun taimaka.


4. Wannan dattijuwar cewa ta ke "mu ma mun taimaka kowa ya taimaka. Jikokinmu ne a cikin makarantun. Wannan bala´in dai shafi mu duka."


A halin da ake ciki bala´in na girgizar ƙasar shi ne batu guda ɗaya tilo a shirye shiryen tashoshin telebijin ƙasar. Su haɗa dai da hirarraki masu sosa rai da aka yi da dangin waɗanda suka rasa ´yan´uwansu da hirarraki da ma´aikatan agaji likitoci da ma´aikatan jiya da kuma zantarwa da shugaba Hu Jintao yayi da waɗanda suka tsallake rijiya da baya a wannan bala´i.

A yau ɗin kuma shugaba Hu ya miƙa godiyarsa ga dukkan ƙasashen da suka kaiwa China ɗauki a wannan lokacin da take juyayin dubun dubatan ´yan ƙasar da suka rasu a girgizar ƙasar.

 • Kwanan wata 19.05.2008
 • Mawallafi Freyeisen, Astrid / Peking (RBB)
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/E2U9
 • Kwanan wata 19.05.2008
 • Mawallafi Freyeisen, Astrid / Peking (RBB)
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/E2U9