Zaman gaggawa kan kasafin kudin Najeriya | Labarai | DW | 08.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman gaggawa kan kasafin kudin Najeriya

Kasa da tsawon awonni 24 da mika kasafi kudin tarayyar Najeriya ga fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, majalisar zartawar kasar ta gudanar da wani taron gaggawa.

Zaman taron da mataimakin shugaban kasar Ferfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta ya bibiyi kasafin kudin daki-daki domin kaucewa aringizo. Ministoci da wasu shugabanin hukumomin gwamnatin kasar na daga cikin wadanda za su yi nazarin kasasfin kafin daga baya a mika shi zuwa ga shugaban kasa domin rattaba masa hannu.

Rikicin aringizo a cikin kasafin kudin ga dukkan alamu shi ne babban dalilin daya tilasta zaman wannan taron da ke zama irinsa na farko. Kasafin kudin na triliyan 6 da miliyan dubu 67 na zama irinsa na farko ga sabuwar gwamnatin da ta zo a a yayin da 'yan kasar ke fama tarin wahalhalu.