1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman farko na majalisar Iraki

Zainab A MohammadMarch 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bu7R

IRAK

A yaune majalisar dokokin Iraki ta gudanar da zamanta na farko tun bayan zabenta a watan disamban daya gabat,sai dai babu wani tudun dafawa da aka cimma a dangane da kafa sabuwar gwamnatin hadin kana kasa,ayayin babu abunda tattaunawar wakilan ya cimma dangane da barazanar fadawa yakin basasa da Irakin ke fuskanta.

Ko a wannan zama daya dauki dan dan lokaci kalilan sai dai aka samu sabanin raayi tsakanin wakilan shia dana sunni da ke wannan majalisar.Ayayinda wasu ke masu raayin rarraba manyan makamai tsakanin kabilun kasar,wasu yan majali na masu raayin cewa harkokin tsaro sune ya dace a mayar da hankali kansu a yanzu a Irakin.A zaman na yau dai yan majalisar sun kawo misalai dangane da cigaban asaran rayuka da akeyi a sassa daban dfaban na kasar ta Iraki,ba tare da yunkurin gano bakin zaren warware ire iren rikicin ba.Prime minista Ibrahin Jaafari,wandfa yan shia suka nada shi a matsayin mai zarcewa kann wannan mukami nasa a karo na biyu ,yace yana da ikon cigaba da rike wannan mukami nasa ba tare da laakari da adawan yan Sunni da kurdawan kasar ba.