1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman dar-dar yayin zaben shugaban Guinea

Mouhamadou Awal BalarabeOctober 11, 2015

Zaben shugaban kasar Guinea na gudana cikin yanayi na fargabar barkewar tashin hankali bayan kashe-kashen da aka fuskanta a ranar Jumma'ar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/1GmHk
Guinea Wahl 2013 Stimmabgabe
Hoto: C.Binani/AFP/GettyImages

A wannan Lahadin ne ake gudanar da zaben shugaban kasa a Guinea Conakry a cikin wani hali na fargabar barkewar tashin hankali tsakanin magoya bayan gwamnati da kuma na adawa. Mutane bakwai ne dai suka rasa rayukansu a ranar Jumma'a da ta gabata yayin tashin hankali da ya barke tsakanin magoya bayan Shugaba Alpha Conde da kuma na madugun 'yan adawa Dalein Diallo.

Shida daga cikin 'yan takara bakwai sun nemi a dage zaben, lamarin da gwamnatin ta ce ba zai yiwu ba. Suna zargin gwamnati da gaza yin sahihiyar rejistar masu zabe da kuma raba katunan zaben yadda ya kamata.

Shugaba Alpha Conde na neman wa'adin mulki na biyu. Ya dare kan kujerar mulki ne a shekara ta 2010 bayan da kasar ta Guinea Conakry ta shafe shekaru da dama karkashin mulkin kama karya na sojoji. Mutane miliyan shida daga cikin al'umma miliyan 12 da kasar ta kunsa ne suka cancanci kada kuri'a