Zaman dar dar a Somalia... | Labarai | DW | 01.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman dar dar a Somalia...

Mdd tace a yan watanni kadan da suka gabata kasar Somalia tafi ko wace kasa fuskantar tashe tashen hankula da kuma rikice rikicen yan tawaye. A tsawon kwanaki uku da suka wuce a cewar Mdd, mutane 88 ne suka rasa rayukan su a birnin Magadishu. Hakan a cewar rahotanni, ya biyo bayan bata kashin dake wanzuwa ne a tsakanin dakarun kutunan Islama da kuma sojin kasar dake samun goyon bayan sojin kasar Habasha.A waje daya kuma, jami´an bayar da agaji sun koka a game da rashin sukunin tafiyar da ayyukan su yadda yakamata. A cewar jami´an, ayyukan nasu na fuskantar koma baya ne, a sabili da yawaitar rikice rikice da kuma tashe tashen hankula.Rahotanni sun ce yanayin ya haifar da saka daruruwan mutane dake neman agaji cikin wani halin na kaka ni kayi.