Zaman dar-dar a Kwango | Siyasa | DW | 20.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaman dar-dar a Kwango

Ana cikin zaman rashin tabbas a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango bayan da wa'adin mulkin shugaba Josephe Kabila ya kawo karshe. Rahotanni sun ce an gudanar da zanga-zanga a wasu biranen kasar.

An dai ji duriyar harbe-harbe na bindigogi a safiyar Talata (20.12.2016) a birnin Lumunbashi birni na biyu ma fi girma na Jamhuriyar Demokaradiyyar ta Kwango wadda ke zaman cibiyar daya daga cikin 'yan takarar adawar kasar a zaben shugaban kasar wato Moise Katumbi. Masu aiko da rahotannin sun ce an kwashe kusan mintoci 20 ana jin karan harbe-harben a birnin inda aka baza jami'an tsaro masu yawan gaske. Jagoran 'yan adawar Etienne Tshisekedi dan shekaru 84 ya yi kira ga al'ummar kasar da kada su amince da gwamnatin Joseph Kabila wacce ya ce ta kasance haramtacciya bayan cikkar wa'adin mulkinsa:

A ranar Litinin din da ta gabata a garuruwa da dama na Kwangon Kantuna da shaguna da ofisoshin da ma'aikatu na gwamnati da masu zaman kansu da kasuwannmi sun kasance a rufe,s hin ko mi ke iya faruwa a yau Talata Mendji wata yar jarida dake birnin Kinsasha ta ce ''bamu san abinda zai faru ba. Gaskiya ne an yitashin hankali bayan da wa'adin Joseph Kabila ya kawo karshe amma kuma a Kinsasha jama'a na cikin shiri sai dai bamu san abinda zai biyo baya ba.''

Josephe Kabila dan shekaru 45 wanda ya hau karagar mulki tun a shekaa ta 2001 ya dage wajen ci gaba da yin mulki duk kuwa da cewar wa'adin mulkinsa ya kammala sannan kuma kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa sake tsayawa takara. Tun a farkon watan Disambar nan ne Cocin Roman Katilika a kasar ya soma jagorantar wata tattaunawa ta neman sulhu tsakanin gwamnatin da 'yan dadwa sai dai ba a  yi nisa ba masu shiga tsakanin suka dakatar da tattaunawar a sanadin cijewar da ta yi.

Sauti da bidiyo akan labarin