Zaman dar-dar a Addis Ababa babban birnin Habasha | Labarai | DW | 05.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman dar-dar a Addis Ababa babban birnin Habasha

Rahotanni daga Addis Ababa babban birnin Habasha sun ce kura ta lafa, amma har yanzu ana cikin zaman dar-dar, kwana daya bayan mutuwar akalla mutane 4 a wata arangama tsakanin ´yan sanda da masu zanga-zanga. Masu zanga-zangar dai na bukatar a sako ´yan adawa da ´yan sanda suka kame. Mutane da dama sun rasa rayukansu sannan wasu daruruwa sun samu raunuka a tashe tashen hankula da aka shafe mako guda ana yi tsakanin jami´an tsaro da masu zanga-zangar nuna adawa da sakamakon zaben ´yan majalisar dokokin da ya gudana cikin watan mayu. A kuma halin da ake ciki kungiyar tarayyar Afirka ta nuna damuwa game da girke dakaru da kasashen Habasha da Eritrea ke yi akan iyakar da ta raba kasashen biyu. A farkon wannan mako jami´an MDD sun nuna fargabar cewa wani sabon yakin kan iyaka ka iya barkewa tsakanin kasashen biyu.