Zaman baƙi a Jamus shekaru 20 bayan faɗuwar katangar Berlin | Zamantakewa | DW | 30.09.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Zaman baƙi a Jamus shekaru 20 bayan faɗuwar katangar Berlin

A ranar 9 ga watan Nuwamba za a yi bikin cika shekaru 20 da buɗe katangar Berlin. Kafofin yaɗa labaru tuni sun fara mayar da hankali kan yadda rayuwar baƙi ta canza a Berlin.

default

Katangar Berlin a 1988

A ranar 9 ga watan Nuwanba za a yi bukukuwan cika shekaru 20 da faɗuwar katangar Berlin, lamarin da ya janyo sake haɗewar Jamus Ta Gabas (JTG) da Jamus Ta Yamma (JTY). To sai dai a wancan lokaci wani ɓangare na wannan al´uma musamman baƙi sun kasance 'yan kallo lokacin bukukuwan faɗuwar katangar, yayin da wasunsu suka shiga cikin halin ƙaƙanikayi sakamakon wannan abin tarihi.

Truong Hanh ɗan ƙasar Vietnam yana dai kantin sayar da kayan lambu a unguwar Prenzlauer Berg dake yankin gabashin Berlin, har yanzu yana tune da lokacin da aka buɗe katangar ta Berlin da yadda a matsayinsa na baƙo a ƙasar JTG yayi tattaki karon farko zuwa JTY.

“Daga nan muka tsallake katangar muka shiga Yammacin Berlin, sannan da yamma muka koma gida. A kullum mun yi ta tsallake katangar a daidai ƙofar Brandenburg, wato inda katangar ba ta da tsayi sosai. Mu kan kwashe tsawon rana a Berlin Ta Yamma kafin mu koma gida da maraice. A gaskiya abin yayi kyau.”

A wancan lokaci Truong Hanh na matsayin ma´aikacin haya a birnin Dresden. Kamar sauran dubban ´yan ƙasarsa ta Vietnam shi ma ya yi aiki a wata masana´anta a JTG, inda ya yi zama a wani ƙaramin ɗaki a wani gidan baƙi. A duk lokacin da suka so shiga Berlin ta Yamma ana hana su tsallake kan iyakar JTG saboda ba su da izinin fita daga ƙasar kasancewarsu ma´aikatan haya a Jamus ta Gabas. To amma Troung da abokansa suna tsallake katangar ta ɓarauniyar hanya suna shiga Yammacin Berlin domin sayen wasu ƙananan abubuwa da ba´a samu a Gabashin Berlin.

“Sau da yawa dai mu kan saye taliya ko miyar kifi. Ba ma iya yin dakon kaya da yawa saboda tsallake katangar da muke yi. A dole muka yi ta yin canjin kuɗi ta bayan fage. Domin idan za ka Berlin Ta Yamma kana buƙatar takardun kuɗi na D-Mark, amma a nan takardun kuɗi na Mark kaɗai muke amfani da su, saboda haka dole ka canza su a kasuwannin bayan fage. To sai dai ba mu da kuɗi da yawa da za mu iya sayen rigunan sanyi ko wandunan zamani. Saboda haka kayan abinci kaɗai muke iya saya.”

Ko shakka babu wannan baƙon ya yi farin ciki da rugujewar JTG. To sai dai fatansa ya kasance ka da ya koma ƙasar ta Vietnam mai bi tsarin gurguzu bayan kwantaragin aikinsa ya ƙare. Burinsa dai ya cika domin shekaru uku bayan haɗewar Jamus, Truong ya samu izinin ci-gaba da zama a Berlin.

A wancan lokaci Berlin ta Yamma ta cike maƙel da jama´a da motoci, inda ake yi ta shagulgula. Dukkan mazauna gabashi da yammacin Berlin sun yi farin ciki ga wannan rana ta faɗuwar katangar. To sai dai ba haka Turkawa mazauna Berlin suka shaida faɗuwar katangar ba. Suat Bakir ɗan kimiyyar tattalin arziki ne kuma masani a fannin zaman baƙi ´yan ƙaƙa-gida, ya ce da yawa daga cikin ´yan ƙasar sun kasance ´yan kallo ne kawai.

“Ba a shigar da baƙi a cikin shagulgulan ba. An kasance ne kamar a wani bikin aure wato inda ake cikin murna da farin ciki. Ɓangarori biyu suna cikin farin ciki wato ɓangaren ango da na amarya da kuma iyalansu, to amma mun kasance tamkar baƙin da ba a gayyata ba. A nan ina mai jaddada cewa Jamusawa ne suka yi bikin amma mu baƙi mun kasance ´yan kallo kawai.”

A ra´ayin Suat Bakir mai shekaru 47, da yawa daga cikin baƙi a wannan lokaci a 1989 sun yi ƙorafin cewa batun shigar da baƙi da ya ɗauki hankali sosai a JTY, ba wanda ya nuna sha´awa a kai, domin Jamusawa sun fi mayar da hankali akan abubuwan da suka shafe su kai tsaye. Nevim Cil masaniyar kimiyyar siyasa ce a birnin Berlin, ta tabbatar da wannan iƙirarin. A lokacin karatun ta na neman digirgir Cil ta ji ra´ayoyin Turkawa kan halin da suka shiga ciki bayan faɗuwar katangar.

“Da yawa daga cikin baƙi matasan da muka yi hira da su, sun shaida mana cewa tun da farko sun ɗauki kan su a matsayin Jamusawa sannan sun yi ƙoƙarin ganin haka ya tabbata wato su zama Jamusawa. Abin nufi dai shi ne za su himmatu wajen koyan harshen Jamusanci, samun abokai Jamusawa da kuma ƙarfafa hulɗa da Jamusawa. To amma bayan guguwar canjin da ta kaɗa ya sa an fuskanci koma-baya ga wannan buri a tsakanin jama´a, domin jama´a ta yi ta ba da muhimmanci ga asalin waɗannan matasa. Hakazalika an juyawa mutanen da suka ɗauki kan su a matsayin wani ɓangare na wannan al´uma, baya. Wannan dai ya kasance wani babban abin takaici.”

´Yar kimiyyar siyasar ta ce har yau Turkawa na ji a zukatansu cewa ba za´a taɓa yin maraba da su a wannan ƙasar kamar yadda aka yi da al´umar tsohuwar JTG ba. Saboda haka yaudara ce kawai da cewa idan suka mayar da himma za su iya sajewa da ´yan ƙasa.

Yayin da ma´aikatan kwantaragi ´yan asalin Vietnam a JTG ke murna su kuwa Turkawa mazauna Berlin Ta Yamma takaicinsu suke nuna. Haka zalika da yawa daga cikin baƙi sun samu kansu a matsayin ´yan kallo lokacin da aka buɗe katangar kamar yadda Tatjana Forner ´yar asalin Rasha dake zaune yanzu haka a Gabashin Berlin ta shaida. Tatjana masaniyar ilimin falsafa ta yi mamaki yadda a wancan lokaci JTG ta yi saurin rugujewa abin da ya buɗe hanyar sake haɗewar Jamus.

“Na yi godiya ga wannan abin domin na shaida wannan abin tarihi da ya faru. Haƙiƙa wannan wata kyauta ce kuma mai ban sha´awa ganin yadda ƙasar ta sake haɗewa.”

Mawallafa: Jens Rosbach / Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmed Tijani Lawal

Sauti da bidiyo akan labarin