1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zama na farko na majalisar Somalia

February 13, 2006
https://p.dw.com/p/Bv8C

Manyan shugabannin kasar Somalia guda 3 sun ce sun sasanta bambance bambance dake tsakaninsu game da guri da kuma ranar da majaslisar kasar zata fara zama.

Wata sanarwa da suka bayar yau,tace shugaba Abdullahi Yusuf,da Firaminista Ali Muhammed Gedi da kakakin majalisa Sharif Hassan Sheikh Aden,sun amince su kawo karshen tafiyar hawainiyan da zaman majalisar yakeyi,inda a yanzu zata zauna a ranar 26 ga watan fabrairu da muke ciki.

Tun ranar asabar Gedi da Aden suke ganawa a akan wannan batu a garin Galkayo dake tsakiyar Somalia.