Zakaran gasar gwanin kwallo na DW a Nijar | Zamantakewa | DW | 13.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Zakaran gasar gwanin kwallo na DW a Nijar

Mika kyauta ga matashin da ya lashe gasar kwallo na DW a jamhuriyar Nijar.

Mahamane Mounkaila Mato da ya samu nasarar gasar gwanin kwallo na DW, wacce sashen wasanni na DW kan tsara ya karbi kyautarsa ta rigar 'yan wasa (Jersey) ta Bayern Munich daga DW.

Isoufou Mamane wakilin Sashen Hausa na DW wanda ke sanye da riga ruwan madara da jar dara, shi ne ya mika wa Mahamane Mounkaila Mato kyautar a ranar Lahadi 12.03.2017, a birnin Tahoua na Jamhuriyar Nijar.