ZAINABAM ABUBAKAR | Siyasa | DW | 24.11.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZAINABAM ABUBAKAR

Wani harin bomb na gefen titi ya ritsa da tawagar motocin dakarun Amurka dake tafiyxa a garin Mosul dake arewacin Iraki,inda guda daga cikin su ya samu matsanancin rauni.Wadanda suka ganewa idanunsu yadda wannan hadari ya auku sun bayyana cewa motar sojojin ta kama da wuta amma nan take dakarun suka rufe hanya domin kada aga me ke faruwa.

A jiya lahadi ne kuma akayi sojojin Amurkan biyu yankan rago a tsakiyar garin na Mosul dake arewacin Irakin,yankin da ake ganin baa cika samun rikicin yan sari ka noke din ba.To sai dai ayayinda ake cigaba da yiwa dakarun mamayen dauki dai dai a Iraki,su kuma a nasu bangaren suna kokarin amfani da kafofin yada labaru wajen tabbatar da hujjarsu na cigaba da kasancewa a wannan kasa.sai dai daidai wannan lokaci dakarun na mamaye tare da gwamnatin da Amurka kewa jagoranci sun fara karaya dangane da mayar da martanin yan kasar ta Iraki,dama wasu dake kai musu irin wadannan hari ba tare da sanin ko su wanene ba.

Bugu da kari majalisar gudanar da Irakin ta sanar da daukan tsauraran matakan yaki da taaddanci musamman adangane da kisan kiyashi da akewa yan Amurka dake kaka gida a Irakin. Shugaban majalisar Jalal Talabani ya fadawa taron manema labaru a Bagadaza cewa daga cikinmatakan da aka dauka harda amfani da hukumomin tsaro tare da amfani da jammiyyun siyasan wannan kasa.Sai dai Talabani wanda ke shugabantan jammiyar Kurdawa ta PUK baiyi karin haske dangane da yadda zasu aiwatar da wannan tsari ba,inda yace a watan gobe ne zaa fara amfani da kafofin yada labarun Irakin wajen kampaign din yaki da taaddanci.ya kara dacewa kashi 10 daga cikin dari na akasarin Irakin ne ke fama da ayyukan yan taadda.

A daya hannun kuma yau ne yan kasar ta Iraski suka fara bukin karamar sallah bayan azumin watan Ramadan,koda yake bukin bai sam,u karrabawa ba kamar yadda aka saba saboda yadda halin rayuka take a wannan kasa,ga kuma dakarun mamaye na cigaba da kasancewa tsakanin jamaa.Dubban alumman musulmi dake Irakin ne suka je hawan idi ayau a masallacin Abu Hanifa,ayayinda karan inginan jiragen yakin Amurka ke shawagi a sararin samaniya,tare da lura da dukkan harkoki dake gudana musamman a dangane da boma bomai da suka tashi a wasu sassan kasar a yau,bayan yankan rago da akayiwa dakarun na Amurka da rana tsaka jiya a tsakiyar garin Mosul da wani kuma daya bakunci lahira tare da raunana wasu biyu a yayinda wani bomb ya tashi dasu a garin Baquba mai nisan km 65 arewacin Bagadaza. Tun bayan hambare gwamnatin Sadam Hussein garin Mosul dake arewacin Bagadazan ya kasance daya daga cikin yankuna dake zama cikin lumana ,amma ayan makonni da suka gabata yankin ya fuskanci rikicin yan yakin sunkuru daban daban,musamman na tashin boma bomai da aka dasa a gefen hanya.