Zagon kasa ga aikin hakar mai a Nigeria | Labarai | DW | 06.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zagon kasa ga aikin hakar mai a Nigeria

Yayin da kungiyar kasashe masu arzikin mai na duniya OPEC ke shirin gudanar da wani muhimmin taro a mako mai zuwa, a birbnin Vienna, a wage guda kuma tsagerun matasan yankin Niger Delta a Nigeria, sun lashi takobin dakatar da hako mai a yankin da kimanin ganga miliyan daya. A can baya, sakamakon hare hare a kan bututun mai ya sanya kasar ta rage yawan man da ta ke hakowa da ganga 445,000. Nigeria dai na hako danyen mai ganga miliyan biyu da rabi a kowace rana. Yan takifen na Niger Delta sun sha nanata kai farmaki a kan rijiyoyin man har sai gwamnati ta biya musu bukatun su.