Zagayowar shekaru biyu da aukuwar igiyar ruwan Tsunami | Labarai | DW | 26.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zagayowar shekaru biyu da aukuwar igiyar ruwan Tsunami

Kasashen nahiyar Asiya masu iyaka da tekun Indiya suna gudanar da bukukuwan tunawa da bala´in igiyar ruwan nan ta Tsunami wadda ta auku shekaru biyu da suka wuce. Wata girgizar kasa mai karfin awo 9 a ma´aunin richter da ta auku a karkashin teku a can kusa da tsibirin Sumatra na kasar Indonesia a ranar 26 ga watan desamban shekara ta 2004, ta janyo igiyar ruwa wadda ta halaka mutane kimanin dubu 230. Lardin Aceh na Indonesia ya bala´in ya fi shafa, inda mutane dubu 167 suka rasu sannan har yanzu dubban mutane ke ci-gaba da zama a gidajen wucin gadi. A kuma halin da ake ciki ana gudanar da wani aikin ceto a yankin bayan wata ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 80 yayin da dubu 100 suka tsere zuwa kan tuddai.