1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Zagayowar Ranar Zaɓen Farko A Jamus ta Gabas

A daidai ranar 18 ga watan maris na shekara ta 1990 ne aka gudanar da zaɓen majalisar dokoki na farko akan tsarin demoƙraɗiyya a tsofuwar Jamus ta Gabas

default

Taya Helmut Kohl nasarar zaɓen farko a Jamus ta Gabas a 1990

Kimanin jam'iyyu talatin da huɗu suka shiga takara. A kuma cikin watan agustan shekarar ta 1990 yankin ya shigo ƙarƙashin tutar Tarayyar Jamus, wanda ta haka zaɓen demoƙraɗiyyar na farko ya kuma kasance shi ne na ƙarshe a yankin na tsofuwar Jamus ta Gabas.

Lamarin dai kamar mutum ya fashe taga ne in ji marabucin adabi Stefan Heym a lokacin da yake jawabi ga dubban ɗaruruwan mutanen da suka hallara a dandalin Alexanderplatz dake birnin Berlin a wajejen ƙarshen shekara ta 1989. Watanni ƙalilan bayan haka guguwar juyin-juya-hali a cikin ruwan sanyi da al'umar Jamus ta Gabas suka gabatar ta share hanyar gudanar da zaɓen demoƙraɗiyya na farko kuma na ƙarshe ga majalisar dokokin yankin. Al'umar Jamus ta Gabas, waɗanda suka saba naƙaltar yaƙin neman zaɓe ta akwatunan telebijin, nan da nan suka wayi gari ana damawa da su.

Ga dai abin da wasu daga cikinsu ke cewa:

"Ba mu san tahaƙiƙanin wanda zamu zaɓa ranar sha takwas ga maris ba..Wani lokaci mutun kan tafa hannunsa yana mamakin ire-iren abubuwan da suke faɗa...Akwai mamaki a game da yadda wasu jami'iyyun ke gabatar da kansu.

A maimakon jam'iyyar haɗin kan ƙasa ta SED da ta saba babakere a al'amuran Jamus ta Gabas an wayi gari jam'iyyu kimanin talatin da huɗu sun shiga takarar zaɓen. Stefan Hilsberg, ɗan jam'iyyar Socialdemocrat, wanda a wancan lokaci ya cimma nasarar shiga majalisar, daga baya ya tunasar da irin ɗoki da murnar da jama'a suka shiga a wancan lokaci.

"Tabbatar da wannan zaɓen da kuma shiga a dama da kai abu ne mai faranta rai matuƙa ainun. An kuma lura da hakan a fuskan illahirin jama'ar yankin, waɗanda nuna alamar cewar kamar dai sun sake ƙwaco wani abu ne da suke mallaka tun da farko."

Kimanin kashi 93% na masu ikon kaɗa ƙuri'a ne suka shiga aka dama da su a wancan lokaci, amma bayan haka ba a sake samun irin wannan adadi a gabacin Jamus ba. Sakamakon zaɓen dai ya zo a ba zata. Domin kuwa 'yan Socialdemocrats da aka daɗe ana hasashen cewar su ne zasu lashe zaɓen, sun tashi ne da kashi 22 cikin ɗari na jumullar ƙuri'un da aka kaɗa, a yayinda jam'iyyar haɗin guiwa don kyautata makomar Jamus ta samu riɓanyen haka. A lokacin da yake waiwayar baya, babban ɗan takararta Lothar de Maiziere ɗan Christiandemocrat cewa yayi:

"A zaɓen na 18 ga watan maris mutane sun ba da goyan baya ne ga wanda ya ƙarfafa manufar sake haɗewar Jamus. A ganina zaɓen na ranar 18 ga watan maris ya zama tamkar wata turba ce ta haɗewar Jamus."

'Yan Christiandemocrats da 'yan Socialdemocrats dai su ne suka yi babakere a yaƙin neman zaɓe sakamakon goyan bayan da suka samu daga ƙawayensu na yammacin Jamus. Kuma jam'iyyar da ta fi ɗanɗana ƙudarta ita ce ta PDS, wadda ta maye gurbin SED ta kuma koma rukunin 'yan hamayya tare da kashi 16 cikin ɗari. A kuma daidai ranar 23 ga watan agustan shekara ta 1990 majalisar dokokin ta Jamus ta Gabas ta tsayar da ƙudurin shiga ƙarƙashin tutar janhuriyar tarayya ta Jamus.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi