Zagayowar ranar 11 ga watan satumba | Siyasa | DW | 09.09.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zagayowar ranar 11 ga watan satumba

A sakamakon mawuyacin hali na kaka-nika-yi da mahaukaciyar guguwar katrina ta haddasa, ba a mayar da hankali sosai ga zagayowar ranar 11 ga watan satumba

Harin 11.09.2001 a cibiyar ciniki ta duniya

Harin 11.09.2001 a cibiyar ciniki ta duniya

‚Yan kunar bakin wake na kungiyar Al-Ka’ida ta Osama Bin Laden sune ke da alhakin wannan danyyen aiki domin adawa da al’amuran kasashen yammaci da kuma kyamar manufofin Amurka dangane da Yankin Gabas ta Tsakiya. Domin mayar da martani akan haka shugaba George W. Bush ya gabatar da matakinsa na murkushe ta’addanci a duniya, wanda a karkashinsa Amurka ta gabatar da yaki kann kasar Afghanistan, kazalika a wani bangaren ta fake da wannan hujja domin kifar da mulkin shugaba Saddam hussein a kasar Iraki. A wancan lokaci shugaban na Amurka ya fito fili ya bayyana cewar al’amura ba zasu taba sake dawowa kamar yadda suka kasance a zamanin baya ba. Alal-hakika kuwa an samu canje-canje masu yawa tun bayan wannan ta’asa ta kisan kiyashi shekaru hudun da suka wuce, inda su kansu Amurkawa suka waye da ainifin halin da ake ciki a wasu sassan duniya dabam, wadanda kafin ranar ta 11 ga watan satumban shekara ta 2001, suka yi watsu da su. Domin kuwa shi ta’addanci, ba a ranar 11 ga satumban shekara ta 2001 ne ya fara ba. An yi shekaru masu yawa ana fama da irin wannan danyyen aiki na kashe-kashen ba gaira a wasu sassa na duniya a kokarin cimma wasu manufofi na siyasa ko ta halin kaka. Amma fa tun da ake ba a taba samun wata kasa da ta ba wa manufar yaki da ta’addanci fifiko a cikin manufofinta ba, tana mai amfani da kalmar yaki kamar dai ana iya amfani da makamai na zamani domin murkushe ‚yan ta’addan. Tankokin yaki da bomabomai da makamai masu linzami ba zasu tsinana kome ba wajen yakar ‚yan sunkuru dake da zazzafan ra’ayi na gani kashe-ni. Duka-duka abin da wadannan makamai zasu tsinana shi ne su hana kungiyoyi irinsu Al-Ka’ida wata kafa a tsakanin jama’a, amma ba zasu iya hana hare-harensu na sare-ka-noke ba. Bugu da kari, ita Amurka ta gabatar wani mataki ne na yaki, wanda a karshe, ita ce kuma zata kwashi kashinta a hannu, saboda ta hada har da mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba. Kazalika kasar ta Amurka tana amfani da matakai na rashin imani a matsayinta na babbar daula kuma ta haka ‚yan kama karya a daya bangaren ke dada samun farin jini tsakanin al’umarsu inda suke batu a game da wani yaki na al’adu. Hare-haren ta’addancin dai ba kawai Amurka ce ke fama da su ba, su ma kasashen Turai kamar Spain da Birtaniya sun fuskanci wannan danyyen aiki, wanda bai bar kowa ba, hatta su kansu kasashen da suka bijire wa Amurka, saboda fafutukarsu ta yada tsarin mulki na demokradiyya zuwa sauran sassa na duniya ko ta halin kaka, wanda kuma ake dauka cewar ba kome ba ne illa wani yunkuri na yada akidojin kasashen yammaci a kasashen da lamarin ya shafa. Kuma ko da yake ana iya madalla ta manufofi na demokradiyya da suka fara bayyana a kasashe kamar Irak da Lebanon da kuma Masar, amma wannan ba abu ne da ya taka kara ya karya ba. A fakaice ma wani yunkuri ne na kara tabbatar da madafun iko a hannun shuagabannin kasashen. Ba shakka an samu canje-canje a cikin shekaru hudun da suka biyo bayan hare-haren a cibiyar ciniki ta duniya, amma ba wani dalili na doki da murna, saboda duniya ba gyaruwa tayi ba, ta kara kutsawa ne cikin yamutsi da hali na rashin sanin tabbas.