1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zagayowar cika shekara da harin kunar bakin wake a London

July 7, 2006
https://p.dw.com/p/BurL

Yau a faɗin ƙasar Britaniya ake bikin tunawa da cika shekara guda da harin Bom ɗin ƙunar baƙin wake da aka kai a hanyoyin sufuri a London wanda ya hallaka mutane 52 tare da jikta wasu mutanen da dama. An shirya gudanar da adduoí na musamman tare da wasu bukukuwan nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukan su. Iyalan wadanda suka rasun za su halarci wani biki da aka shirya a dandalin Regents inda zaá ambaci sunaye daya bayan daya na waɗanda suka rasu a harin bom din. Magajin garin birnin London Ken Livingstone da sakatariyar kula da aládu Tessa Jowell tare da kwamishinan harkokin sufuri Peter Hendy za su ƙaddamar da bikin zagayowar ranar tare da sanya furanni a tashar jirgin ƙasa na King Cross. Za kuma a cigaba da sanya wasu furannin a dandalin Tavistock da karfe 9:47 daidai lokacin da ɗaya daga cikin yan kunar bakin waken Hasib Hussain ya tada nakiyar dake jikin sa wanda ya tarwatsa wata motar safa ɗauke da jamaá. Zaá yi shiru na minti biyu a fadin ƙasar Britaniya baki ɗaya da karfe goma sha biyu na rana domin karramawa ga mamatan.